(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya zanta da takwaransa na kasar Turkiya Mevlut Cavusoqlu ta wayar tarho a jiya Jumma’a.
Kamfanin dillancin labarai na “Iran Press” ya bayyana cewa ministocin biyu sun tattauna dangane da rikicin da ke faruwa a yankin, musamman na arewacin kasar Siriya.
Iran Press ya kara da cewa kafin haka dai Zarif ya kira takwarorinsa na kasashen Rasha, Siriya da kuma Iraqi ta wayar tarho, inda suka zanta dangane da rikicin na arewacin kasar Siriya.
Majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa ministan zai ci gaba da tuntubar wadannan kasashe domin ganin an tsagaita bude wuta a fafatawar da sojojin kasar Turkiya suke yi da wasu kurdawan kasar Siriya a arewacin kasar.
A ranar Larabar da ta gabata ce gwamnatin kasar ta Turkiya ta fara kaddamra da hare-hare a kan mayakn kungiyar kurdawa ta SDF a arewacin kasar Siriya.
Kasar Turkiyya tana daukar kungiyar SDF a matsayin yan ta’adda, domin irin dangantakar da take da ita da kungiyar PKK mai son ballewa daga kasar ta Turkiyya. Kuma ta sha alwashin fitar da mayakan kungiyar daga arewacin kasar ta Siriya.
.........
340